Domin kawowa al’umma saukin rayuwa, Gwammatin tarayya ta sanar da shirin cire harajin VAT daga shigo da kaya da hukumar Kwastam ke karba akan kayan abinci na tsawon watanni 6.
Gwammati zata dauki wannan mataki ne dan magance matsalar hauhawar farashin kayan abinci.
Yanzu haka an aikawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da rahoto kan wannan lamari dan ya duba ya saka masa hannu.
Kayan da za’a cirewa harajin sun hada da kayan abinci, magunguna, abincin kaji, Fulawa da sauransu.
Da yawan ‘yan Najeriya dai na kukan tsadar rayuwa, abin jira a gani shine idan wannan mataki zai haifar da da me ido.