Tuesday, April 29
Shadow

A kara yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu uzuri, duk matsalolin da ake fama dasu yanzu ya gajesu ne daga Gwamnatin Buhari>>Tsohon Gwamnan Kano Ganduje

Shugaban jam’iyyar APC kuma tsohon Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya baiwa ‘yan Najeriya hakuri inda yace su ci gaba da baiwa gwamnatin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu uzuri.

Yace matsalolin da ake fama dasu, Tinubu ya gajesu ne daga Gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Ganduje ya bayyana hakane a wajan taron kaddamar da wani Littafi kan cika shekara 1 da gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta yi akan mulki.

Ganduje ya kara da cewa, matakaj da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yake dauka na kawo gyara aun fara nuna alamar nasara.

Karanta Wannan  Shugaba Bola Tinubu ya umurci Ministan kuɗi, Wale Edun, da ya fito da abubuwan da za a kashe akan sabon mafi ƙarancin albashi cikin kwanaki biyu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *