Friday, December 5
Shadow

Bankunan Najeriya zasu fara cajin Naira 6 akan kowane sakon balance da suka aikawa mutane daya yau dinnan

Bankunan Najeriya zasu fara karbar Naira 6 akan kowane sako da suka aikawa Kwastoma daga yau, Ranar Alhamis.

Hakan na zuwane bayan da kamfanonin sadarwa a Najeriya suka karawa mutane kudaden kira dana data.

Kudin da ake cirewa akan sako an karashi da kaso 50 cikin 100 inda a yanzu ake cajin Naira 6 maimakon Naira 4 a baya.

Bankuna da dama sun aikawa kwastomominsu da abokan huldarsu sakonni dan sanar dasu sabon tsarin cajin kudin.

Shin haka za’a yi ta kakabawa mutane haraji ba tare da suna magana ba?

Karanta Wannan  Dole Tinubu ya dauki mataimaki Kirista ko kuma ya fadi zabe a 2027>>Inji Wata Kungiyar Kirista

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *