Friday, December 5
Shadow

Shugaban Kungiyoyin da suka kai korafi a Abinciki tsohon Shugaban NNPCL, Mele Kolo Kyari ya janye bukatar binciken saidai abokan Gwagwarmayarsa sun ce basu tare dashi saboda an sallameshi ne

Shugaban Kungiyoyin gwagwarmaya da suka hada kai suka kai bukatar a binciki tsohon shugaban kamfanin man fetur na kasa, NNPCL, Mele Kolo Kyari ya je ya janye bukatar binciken.

Kungiyoyin sun ce basa tare da shugaban nasu me suna Kabir Matazu.

A wata sanarwa da sakataren kungiyoyin me suna Moses Okino ya fitar, yace Matazu ya yaudaresu da cin amanarsu.

Kungiyar tace dama can akwai wasu na hannun damar Mele Kolo Kyari dake ta son su hana binciken me gidan nasu.

Yace dan haka abinda Matazu yayi ba da yawun kungiya yayi ba yayi ne shi kadai bisa radin kansa.

Yace Matazu bai tuntubesu ba dan haka suna kyautata zaton kudi aka bashi.

Karanta Wannan  Labari Me Dadi: Makamin dake tare makamai da kakkabo jirage na kasar Iran ya dawo aiki bayan da Israyla ta musu kutse

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *