Friday, December 5
Shadow

Mu a Arewa muna sayarwa da ‘yan Kudu gidaje da Filaye amma mu basa sayar mana a yankinsu>>Kungiyar ACF ta koka

Kungiyar Tuntuba ta Arewa me suna ACF ta bayyana cewa, abin takaici ne ya da ‘yan Arewa a kudancin Najeriya ba’a sayar musu da gidaje da Filaye.

Amma nan a Arewa ‘yan kudu na ta mallakar gidaje da filaye.

Shugaban kwamitin amintattu na kungiyar, Alhaji Bashir Dalhatu ne yayi wannan kirafi inda yace ya kamata a jihohi 19 na Arewa a fito da sabon tsarin mallakar fili da gida dan magance wannan matsala.

Yace musamman a jihohin Inyamurai basa sayarwa da ‘yan Arewa fili.

Yace idan ba’a tashi tsaye aka magance wannan matsala ba, muna ji muna gani zamu sama bamu da fili ko gida a garuruwan mu duk baki sun saye.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Ba yaran nan kadai, har iyayensu ya kamata Shugaba Tinubu ya karramasu>>Inji Sheikh Gadon Kaya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *