
Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja ya ƙaryata rade-radin da ake cewa su na zaman doya da manja da mataimakin sa, Yakubu Garba.
Bago ya tabbatar da cewa lafiya lau ya ke zaune da mataimakin na sa.
“Ba wanda zai iya raba ni da mataimaki na. Mu na zaman lafiya kuma mu na aiki tare lafiya. Dukkan mu kuma mu na kokarin wanzar da zaman lafiya a tsakanin mu,” in ji Bago.