Saturday, December 13
Shadow

Ka jawa Danka kunne yana wuce gona da iri>>Atiku ya gayawa Shugaba Tinubu bayan da aka zargi Seyi Tinubu da lakadawa shugaban Daliban Najeriya dukan kawo wuka

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya jawo hankalin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya jawa iayalinsa musamman dansa, Seyi Kunne.

Atiku yace Najeriya ba kayan Tinubu bane kasa ce ta al’umma dan haka bai kamata a bar dan shugaban kasar yana abinda yake ba na yawo yana nemawa mahaifinsa goyon baya ba.

Atiku yace ya zama wajibi a binciki zargin da shugaban kungiyar daliban Najeriya ya yiwa Dan shugaban kasar dan gano gaskiya.

Atiku yace kuma ko me ya faru da Shugaban daliban ba zasu amince ba zasu tsaya mai.

Yace abin takaici ne ace irin wannan abin yana fitowa daga iyalin shugaban kasa.

Karanta Wannan  Idan Tinubu ya sake cin zabe, Najeriya ba zata kai Labari ba, Inji Malam Nasiru Ahmad El-Rufai

Atiku yace wannan abu ne da ba za’a amince dashi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *