Friday, December 5
Shadow

Za mu ƙwato duka dazukan Najeriya daga hannun ɓata-gari -Tinubu

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya tabbatar da cewa gwamnatinsa na ƙoƙarin ƙwato duka wurare da dazukan ƙasar da ƴanbindiga ke ɓuya, ta hanyar girke sabbin dabaru na zamani domin yaƙi da ta’addaci da ƴan fashin daji.

Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga jagororin jihar Katsina a lokacin liyafar cin abincin dare da aka shirya masa a gidan gwamnatin jihar ranar Juma’a.

”Dangane da matsalar tsaro, matsala ce da ta addabi ƙasarmu’, kuma na yi magana da sojoji, na tabbatar musu cewa za mu yi duk mai yiwuwa don kawo ƙarshen matsalar ƴanbindiga”, in Tinubu.

“Za mu samar da kayan aiki na zamani domin ƙwace duka dazukan ƙasarmu daga hannun miyagu, matsalar tsaro ta shafi duka Najeriya ne ba wani yanki ba, kuma mun sani cewa indai muna so ƙasarmu ta ci gaba to dole mu kawar da matsalar tsaro a Najeriya,” in ji shugaban ƙasar.

Karanta Wannan  Ƴan Najeriya sama da miliyan 28 ba sa mu'amulla da bankuna - CBN

Haka kuma Shugaba Tinubu ya tabbatar da tallafa wa rayuwar waɗanda ayyukan ta’addanci ya shafa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *