Wednesday, November 12
Shadow

Ji yanda aka kama Sojoji 2 na taimakawa ‘yan tà’àddà a jihar Borno

Hukumar sojojin Najeriya ta sanar da kama wasu mutane 4 dake kaiwa ‘yan ta’adda kayan masarufi, biyu daga cikin wadanda aka kama din sojoji ne.

Sanarwar tace an yi bincikenne a tsakanin ranar 26 ga watan Afrilu zuwa 29 ga watan kuma an yi bincikenne a kananan hukumomin Bama, Kukawa, da Madagali na jihar Borno.

Kakakin sojin, Major General Markus Kangye ya tabbatar da hakan inda yace abin takaici ne irin wannan cin amana.

Ya jawo hankalin kwamandojin yaki dasu saka ido dan lura da sojoji masu irin wannan hali inda ya gargadi sojojin da kai kansu ga irin wannan hanya ta halaka.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Sanata Abdul Ningi ya zama sanata daya Tilo da yace bai yadda a baiwa Gwamnatin Tinubu damar ciwo bashin Dala Biliyan $21 saboda akwai rufa-rufa a lamarin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *