Friday, December 5
Shadow

Dole mu magance matsalar tsaro idan muna son masu zuba hannun jari su shigo Najeriya>>Shugaba Tinubu

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, dolene gwamnati ta zage ta magance matsalar tsaro idan tana son masu zuba hannun jari su shigo Najeriya.

Shugaban ya bayar da tabbacin Gwamnati na kwato garuruwan dake hannun ‘yan ta’adda musamman a Arewa maso gabas.

Shugaban ya bayyana hakane yayin ganawa da dattawa jihar ta Katsina a ziyarar da ya kai jihar inda yayi Alwashin yin amfani da na’urorin zamani da sauran kayan aiki na zamani dan magance matsalar garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro.

Shugaban yace babu ‘yan kasuwar da zasu je inda babu tsaro su zuba hannun jari, dan haka yace zasu hada hannu da gwamnatoci a kowane matakai su magance matsalar.

Karanta Wannan  Dan Nijeriya Na Farko Da Ya Fara Tuka Jirgin Ruwan Ýàķi A Kasar Amurka, Kaftin Kelechi R. Ndukwe Ya Samu Karin Girma Daga Kaftin Zuwa Kwamanda

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *