Saturday, December 13
Shadow

Mu Makafine, Kwankwaso ne jagoranmu, Duk inda ya koma zamu bishi>>Inji Shugaban NNPP na Kano, Hashim Dungurawa

Shugaban jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano, Hashim Dungurawa ya bayyana cewa, duk inda Kwankwaso ya tafi suna tare dashi.

Ya bayyana hakanne a yayin ganawa da manema labarai na jaridar Leadership a yayin da ake tambayarsa game da yiyuwar komawar Kwankwaso wata jam’iyya.

Yace su dukansu makafi ne Kwankwaso ne jagoransu dan haka duk inda ya tafi zasu bishi.

Yace duk abinda Kwankwaso ya musu daidai ne dan haka su basu da zabi sai nashi, idan ya canja jam’iyya zasu bushi.

Karanta Wannan  Nifa dama ko da Ina APC munafurtarsu nake, Kuma APC din ce ta koyamin Munafurci a siyasa>>Inji Babachir David Lawal

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *