
A ranar Asabar din data gabata ne aka daura auren diyar Gwamnan jihar Katsina, A’isha Dikko Radda da Angonta, Usma Ahmad.
Bikin Yayi Armashi, hadda Shugabab kasa, Bola Ahmad Tinubu ya damu halarta.
A ci gaba da shagalin Bikin, Matan Gwamnoni musaman na jihohin Arewa sun halarci wajan wannan daurin aure.
A wani Bidiyo dake ta yawo a kafafen sada zumunta, an ji yanda ake kashe kudi sosai a wajan bikin wanda hakan yasa mutane da yawa kokawa.
Wasu sun ce mutanen jihar Katsina a wannan watan babu Albashi.
Wasu na ganin a yayin da mutane ke fama da matsin rayuwa da kuma matsalar tsaro wannan bikin na kece raini bai dace ba.