
Babban malamin Addinin Islama, Sheikh Ibrahim Maqari ya jawo hankalin mutane akan tara ‘ya’ya.
Yace a baya mutane na haihuwar ‘ya’ya talatin saboda akwai wadatar gurin zama kuma a wancan lokacin ba sai an saka yaro a makaranta ba.
Yace amma yanzu Rayuwa ta canja, irin wancan abin ba zai yiyu ba.
Saidai malam yace irin mutanen mu na da wahalar canjawa akan wani abu da suka saba dashi.