Saturday, December 13
Shadow

Robert Prevost ne sabon fafaroma

Fadar Vatican ta sanar da cewa Robert Prevost ne sabon fafaroma, wanda zai maye gurbin Fafaroma Francis.

Shi ne fafaroma na farko daga ƙasar Amurka wanda zai jagoranci cocin na Katolika na duniya.

Zai yi amfani da sunan Leo a muƙamin – wanda shi ne fafaroma na 14 da ya yi amfani da sunan (Pope Leo XIV).

Sabon Fafaroman mai shekara 69 ya shafe shekaru yana ayyukan addini a ƙasar Peru.

A watan Satumban 2023 ana naɗa shi a muƙamin babban limamin Cocin Katolika wato ”Cardinal’.

Ana kallon Robert Prevost a matsayin mutum mai matsakaicin ra’ayin.

Za mu ci gaba da sabnta wannan labari…

Karanta Wannan  An zargi cewa An fifota baiwa Adam A. Zango kulawa fiye da sauran wadanda suka yi Hadari tare a Asibiti inda aka bar su duk da sun fi shi jin jiki, har daya ta rasu daga ciki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *