Friday, December 12
Shadow

An kama mahaifi da zargin yiwa ‘ya’yansa mata Fyàde

Rahotanni daga jihar Legas na cewa, ‘yansanda a jihar sun kama wani uba me suna Best Orji dan kimanin shekaru 39 da zargin yiwa ‘ya’yansa fyade.

Mahaifiyar yaran ce ta kai korafi wajan ‘yansandan inda tace ya aikata lamarin a yayin da yaran ke da shekaru 12 da 14.

Kakakin ‘yansandan jihar, (PPRO),CSP Benjamin Hundeyin ne ya tabbatar da hakan a sanarwar da ya bayar ga manema labarai.

Yace sun kama Best Orji zasu gurfanar dashi a gaban kuliya.

Karanta Wannan  Dangote ya nanata cewa, yana da man fetur din dake iya wadatar da Najeriya duk da 'yan kasuwar man sun ce ba gaskiya bane

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *