Saturday, December 13
Shadow

Mun Gano Tabbas ‘yan Tà’àddà na Amfani da Jirage marasa matuka irin na kasashen Israela da Ukraine>>Sojojin Najeriya suka koka

Rundunar soji ta Operation Hadin Kai ta koka da yanda tace masu ikirarin Jihadi na Kungiyar B0k0 Hàràm na amfani da jirage marasa matuka dan kai musu hari.

Rundunar tace irin wannan hare-haren na da wahalar ganowa da dakilewa musamman ta hanyar amfani da hanyoyin da aka saba wadanda ba na zamani ba.

Shugaban Rundunar, Major General Abdulsalam Abubakar ne ya bayyana hakan a wajan wani taro a Maiduguri.

Yace wasu daga cikin jiragen marasa matuka da kungiyar ke amfani dasu na kama da irin wadanda ake amfani dasu a kasashen Israela da Ukraine.

Dan haka ya jawo hankalin sauran ‘yan kungiyar dasu tuba su mika kansu ga jami’an tsaro kamar yanda ‘yan uwansu ke yi kuma ana karbar su tare da cin zarafi ba.

Karanta Wannan  Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan na shirin komawa jam'iyyar ADC

Saidai yayi gargadin wadanda suka ki amincewa su mika kansu, zasu fuskanci kisa

Saidai yace duk da wadannan sabbin dabarbarun na ‘yan kungiyar ta B0k0 hqrqm, gwiwar sojoji bata yi sanyi ba inda yace suma suna fiddo da sabbin dabaru na tunkarar Kungiyar

Yace Najeriya zata yi nasarar yakar ta’addanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *