
An ga wadannan hotunan a sararin samaniyar kasar Greece.
Da farko idan mutum ya kalla, zai yi tsammanin AI ne, amma kafofin yada labarai da yawa irin su Beauty of Planet Earth dake wallafa labarai da hotunan ababen kayatarwa a Duniya sun tabbatar da faruwar lamarin.
Saidai masana kimiyya sunce wannan ba wani abin tashin Hankalo bane, tana iya yiyuwar tauraron dan Adam ne rana ta haskashi shine hasken ya hasko cikin Duniya.
lamarin ya farune ranar 14 ga watan Mayu.