
‘Yan wasan Real Madrid 4 ciki hadda Raul Asencio zasu iya fuskantar hukunci bayan yada Bidiyon badala da wasu mata biyu ciki hadda wata karamar yarinya wadda shekarunta basu kai 18 ba.
Alkalin dake shari’ar yace ya kammala nazarin Bidiyon wanda aka dauka wani wajan shakatawa.
Alkalin yace matan dake cikin Bidiyon daya shekarunta 18 dayar kuma shekarunta 16.
Alkalin yace laifukan da ake zargin ‘yan wasan dasu sune yada Bidiyon da aka dauka a sirce ba tare da izinin wadandake cikin Bidiyon ba da kuma amfani da karamar yarinya