
Babban malamin Addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya soki kasashen Larabawa inda ya kirasu da munafukai saboda yanda suka tarbi shugaban kasar Amurka, Donald Trump suka bashi kudade na fitar hankali dan ya je ya zuba jari a kasarsa.
Kasashen da Trump ya je sune Saudiyya, Qatar, da UAE.
Sheikh Gumi yace wannan kudade da suka baiwa Amurka, kamar sun baiwa Israela ne yace dan ba zaka raba Israela da Amurka ba.
Yace malaman kuma da suka yi shiru to suna da raunin Imanine.