Wata budurwa me suna Ginika Judith Okoro ta mutu a dakin saurayinta bayan da ta kai masa ziyara.
Budurwar wadda malamar Jinya ce shekarunta 22 da haihuwa.
Lamarin ya farune a Ezeogba dake Awaka ta karamar hukumar Owerri North a jihar Imo.
Iyayen budurwar tuni suka nemi hukumomi da su shiga lamarin dan binciko dalilin mutuwar diyar tasu.
Mahaifiyar budurwar, Caroline Nneji ta koka inda tace ita kadai ce diyarta.