
Wani tsohon sojan Najeriya wanda ya ajiye aikin da karfinsa me suna Abubakar Afan ya bayyana cewa an masa tayin zuwa kasar Rasha dan ya tayasu yaki da Ukraine a bashi Naira Miliyan 21 amma yaki.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a kafar Punchng inda yace dalilinsa na kin zuwa shine yasan addinin musulunci ya hana yin yaki saboda kudi, yace idan ya mutu bai san matsayinsa a wajan Allah ba.
Yace sannan akwai abokansa da sukewa Ukraine yaki bai san yanda zai yi ba idan ya je shi kuma yanawa Rasha yaki, shin zai je ya kashe abokan nasa ne?
Yace rayuwarsa ta fi kudin muhimmanci inda yace matarsa ma tace masa bata yadda yaje ba tunda dai basu rasa komai ba.
Yace a yanzu haka ya samu wani aiki ne a kasar Egypt inda yake can yayin da ya bar matarsa a gida Najeriya.