Friday, December 5
Shadow

Nan ba Najeriya ba ce”: Jami’ian tsaron fadar Vatican sub hana Seyi shiga wajen taron Tinubu da Fafaroma

“Nan ba Najeriya ba ce”: Jami’ian tsaron fadar Vatican sub hana Seyi shiga wajen taron Tinubu da Fafaroma.

Seyi Tinubu, ɗan Shugaba Bola Tinubu, ya kasance cikin jerin waɗanda su ka raka shi zuwa bikin rantsar da Fafaroma Leo XIV a ranar Lahadi.

Jaridar Daily Trust ta rawaito muhimman abubuwan da suka faru a wajen bikin, ciki har da ganawar da shugaba Tinubu ya yi da Peter Obi, ɗaya daga cikin manyan abokan hamayyarsa a zaɓen 2023.

https://twitter.com/harreceipts/status/1924155639275659456?t=qnZ8k_3TtTZ2l29ng8GJbQ&s=19

Obi, wanda ya zo na uku a zaɓen, ya doke Tinubu a jihar Legas — inda Shugaba Tinubu ke da rinjaye tun dawowar dimokuraɗiyya a Najeriya a 1999.

Daya daga cikin abubuwan da suka jawo hankali a tafiyar zuwa birnin Vatican ita ce mu’amalar da ɗan Shugaban ƙasa, wanda ke da ƙarfi a gida, ya yi da jami’an tsaron Paparoma.

Karanta Wannan  Shugaba Tinubu yayi Allah wadai da Kàshè-Kàshèn da suka faru a Najeriya bayan ganawa da shuwagabannin tsaro

A cikin wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, an ga Seyi yana kokarin isa wurin mahaifinsa, amma wani jami’in tsaro da ba cikin kakin soja ba ya dakatar da shi cikin natsuwa.

A lokacin da lamarin ya faru, Shugaban Najeriya na gaisawa da Paparoma.

Seyi, wanda ke sanye da baƙin kaya irin na mahaifinsa, ya nemi kusantar shugaban, amma jami’in tsaron ya hana shi.

Sai dai bayan wasu sa’o’i, wani sabon bidiyo ya bayyana inda aka ga Seyi yana cin abinci tare da wasu manyan jami’an cocin Katolika na Roma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *