
Matatar man Dangin ta sha Alwashin ci gaba da rage farashin Man fetur duk da yana tashi a kasuwannin Duniya.
Matatar tace tana ci gaba da rage farashin man ne saboda amincewa da ta rika sayen danyen man fetur din da kudin Naira.
Tace tana godiya ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya amince da yin hakan, kamar yanda wakilin matatar me suna Anthony Chiejina ya tabbatar.
Matatar tace zata ci gaba da goyon bayan karfafa ci gaban tattalin arziki Najeriya da kuma tabbatar da saukin man fetur.