
Wata matashiya me suna Miss Zainab Muhamadu a jihar Zamfara ta yi ridda ta koma Kirista inda Tuni aka kai ta Kotun shari’ar Musulunci a jihar.
Zainab ta zama Kirista ne bayan da ta hadu da wani dan bautar kasa me suna Pastor Samuel da aka kai shi aiki jihar.
Sun shaku sosai har daga karshe ya mayar da ita Kirista.
Saidai Tuni an kamata inda a ranar juma’ar nan me zuwa za’a fara mata shari’a a kotun musulunci dake jihar Zamfara.
Saidai tuni lauyoyi da kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun taso inda suke cewa ba’a mata adalci ba, tana da ‘yancin yin duk addinin da take so.