
Rahotanni na kara bayyana dake tabbatar da alaka me karfi tsakanin Atiku Abubakar da Peter Obi ta kullu.
Rahotannin sun ce, duka bangarorin sun saka hannu a wata yarjejeniya da suka akince da ita.
A tafiyar dai akwai tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai da Tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi da sauransu.
Hakanan rahoton yace sun kuma amince da komawa jam’iyyar ADC da kuma saka kudi dan gyara jam’iyyar.
Saidai duk da El-Rufai shi yana SDP ne, rahoton yace da zarar an kammala shirya komai, za’a sanar da kulla alaka tsakanin SDP da ADC din.
A bangaren APC kuwa, sakataren jam’iyyar Ajibola Basiru ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu shine uban hada kan al’umma kuma suna da yakinin shi zai lashe zaben shekarar 2027.