Tun bayan fashewar Notcoins, matasa a Najeriya suka mayar da hankalai wajen yin mainin, domin tara maki ko ‘points’ a cikin manhajojin da suke amfani da su a wayoyinsu.
Daga lokacin ne kuma harkar kirifto ke ƙara samun karɓuwa a Najeriya, inda a kowace rana ake samun ƙaruwar ɓullar sabbin shafukan mainin da ke alƙawarta samar wa mutane kuɗi.
Masu amfani da shafukan ko manhajojin kan yi ta taɓa sikirin ɗin wayarsu domin samun wani maki da ake kira ‘points’, wanda za a iya canjawa zuwa kuɗi ”idan ta fashe”.
A yanzu akwai sabbin manhajojin waya da dama da ake amfani da su domin samun kuɗin.
Fitattu daga ciki sun haɗa da Notcoins da Tapswap da Hamstar Kombat da Poppo da sauransu.
Yayin da wasu mutane ke darawa saboda kuɗin da suka ce sun samu sakamakon fashewar Notcoins, wasu kuma sun ce har yanzu suna zaman jiran fashewar nasu kuɗin kirifton, domin kwasar ganima.
Inda ake ganin mutane cikin rukunin shekaru daba-daban suka koma yin mainin, a wuraren hirarrakin jama’a, ko kasuwanni ko wuraren sana’o’i da dama da nufin samun kuɗi.
Mafiya yawan waɗannan manhajoji daga shafin Telegram ake sauke su, yayin da wasu kuma ake sauke su daga rumbun sauke manhajoji na manyan wayoyi.
Dole ne sai mutum ya sauke shafin Telegram a wayarsa kafin ya iya amfani da manhajojin.
Wannan ita ce babbar matsalar, kasancewa mafi yawa ba a san masu shafukan ba, kamar yadda Ejike Okonkwo – wanda ya shafe kusan shekara 10 yana harkar kirifto – ya shaida wa BBC.
Okonkwo ya ce akwai hatsari mai yawan gaske tattare da yin rajista a wasu shafukan na kirifton da ba a san masu su ba.
”Hatsari na farko shi ne kasancewar dole sai ta shafin Telegram ake iya samun damar shiga manhajojin”, in ji Okonkwo.
“ShafinTelegram shafi ne da kowa ke da ‘yancin yin abin da ya ga dama, don haka komai zai iya faruwa a shafin. Mutum zai iya buɗe shafi a dandalin ba tare da wata tantancewa ba, sannan zai iya ɗaukar bayanan duka hirarrrakin da ya yi da mutane a dandalin a kowane lokaci. Shafi ne da zaka iya cewa masu kutse ke da damar yin abin da suka ga dama a kowane lokaci,” in ji shi.
Hatsarin faɗawa laifukan intanet
Okonkwo ya ce akwai hatsarin tafka asarar kuɗi, duk da cewa a yanzu manhajojin ba su buƙatar masu amfani da su su saka kuɗi kafin samun damar yin mainin.
“To amma a ƙoƙarin mai amfani da shafin wajen cire kuɗin da ya samu, manhajar kan buƙaci ya aika da wallet ɗinsa, kuma hakan ka iya zama hatsarin rasa duka kuɗin da ka samu, saboda ba ka san abin da zai faru ba idan ka tura”, in ji shi.
“Haka kuma a wasu lokutan sukan buƙaci ka biya wasu kuɗi domin su ninka maka makinka ‘points’. Kuma fa ka tuna wannan kuɗi ne da ba a lissafa su cikin ‘exchanger’ ba, zai iya kasancewa har abada ma ba za a lissafa shi ba, to ka ga ashe kuɗinka sun bi shanun sarki kenan”.
Yayin da mutane ke amfani da shafukan da nufin samun kuɗi, akwai abubuwa da dama da ake buƙatar su yi, kamar sake wallafa saƙo a shafukan sada zumunta, ko su danna alamar ‘Like’ ko shiga wani links da sauransu.
“Mafi yawan matasanmu ba ma sa kula da karanta ƙa’idojin kowane manhaja domin gane cewa sake wallafa saƙon ake so su yi, ko kuwa Like ake so su danna, idan Like ake so su danna, to fa idan saƙon na ɗauke da wani laifi, su ne za su faɗa komar jami’an tsaro”.
Illar amfani da VPN
Ejike Okonkwo ya ce shafukan kirifto na bayar da kuɗi gwargwadon inda mai amfani da shafin yake.
A wasu lokutan, masu amfani da shafin a Turai ko Amurka na samun kuɗi fiye da ‘yan Afirka ko da sun yi abu iri ɗaya, hakan ne ya sa wasu masu amfani da shafukan ke sauke manhajar da ke sirrinta inda mutum yake, wato VPN, domin nuna cewa ba a Afirka suke ba.
“Kuma mafi yawan manhajojin VPN na da hatsarin amfani, saboda sukan ɗauki muhimman bayanan masu amfanni da su, wanda kuma daga ƙarshe ba a san abin da hakan zai haifar ba”.
Kuma kasancewar yadda ake amfani da shafin ko da cikin talatainin dare ne domin tara ‘points’ ”Haƙiƙa irin waɗannan manhajoji na da hatsari,” in ji Okonkwo.
Masanin Kirifton ya kuma ce wasu shafukan kirifton kan yi amfani da salon mainin ɗin domin samun shahara tsakanin mutane, ba tare da sun biya mutane kuɗi ba.
Ya ci gaba da cewa in ma za su biya to kuɗin ba su taka kara suka karya ba, idan aka kwatantan da lokacin da suka ɓata a kan wayoyinsu.