Friday, December 5
Shadow

Majalisar Wakilan Najeriya ta buƙaci gwamnati ta ceto ƴan ƙasar da ke maƙale a Saudiyya

Majalisar Wakilan Najeriya ta buƙaci gwamnati ta ceto ƴan ƙasar da ke maƙale a Saudiyya.

Majalisar Wakilan Najeriya ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta ceto ƴanƙasar da ke maƙale a Saudiyya sakamakon sabbin sauye-sauyen dokokin ayyukan ƙwadogo da hukumomin Saudiyya suka bijiro da su.

Dan majalisar wakilai daga jihar Kano, Hon. Muhammad Bello Shehu ne ya gabatar da udurin a yayin zaman majalisar na ranar Laraba.

A baya-bayan nan ne dai hukumomin Saudiyya suka bijiro da wasu sauye-sauye kan dokokin da suka shafi ayyukan baƙi a ƙasar, ciki har da daina sabunta takardun izinin aiki a ƙasar ga wasu mutanen.

Hon. Muhammad Shehu ya ce sauye-sauyen sun tilasta wa wasu ƴan Najeriya da dame da ke zaune a Saudiyya rasa ayyukansu, yayin da wasu ke fuskantar tsadar kuɗin sabunta takardunsu.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Wata Sabuwa ana rade-radin wani babban dan siyasar Najeriya dan luwadi ne, ya mayar da martani

“Ɓangaren zartarwa ta hannun ma’aikatar kula da harkokin ƙasashen waje ba su tuntuɓi hukumomin Saudiyya kan wannan batu ba da nufin samar wa ƴanƙasarmu sauƙi, ko yin wani shiri na kwaso mutanen domin maido su Najeriya ba”, kamar yadda ya bayyana.

Haka kuma ɗan majalaisar ya yi kira ga hukumomin Saudiyya ta sassauta tare da yin la’akari ga mutanen da ke da sha’awar komawa gida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *