
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa shi Madugune wanda ya san hanya dan haka yayi kira ga ‘yan Najeriya da su bishi ya kaisu Tudun Mun tsira.
Shugaban kasar ya bayyana hakane a waja wani jawabi da yayi ga ‘yan jam’iyyar APC a babban taron da jam’iyyar ta gudanar.
Hakanan yace masu kukan za’a mayar da Najeriya jam’iyya daya yace mutane ne suna cikin jirgi suna ganin zai nutse shiyasa suke tserewa.