
Jam’iyyar APC reshen jihar Kebbi sun bayyana shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a matsayin zabinsu a shekarar 2027 sannan Gwamna Nasiru Idris a matsayin zabinsu na dan takarar gwamna a jihar.
Sun cimma wannan matsaya ne bayan zaman da suka yi na musamman da ya faru a Birnin Kebbi na masu ruwa da tsaki a jam’iyyar.
Daya daga cikin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, Abdullahi Idris Zuru ya tabbatar da hakan.
Hakana zaman yayi maraba da tsaffin sanatocin jihar karkashin jam’iyyar PDP da suka koma APC wadanda sune Senator Muhammad Adamu Aliero (Kebbi Central), Dr. Yahaya Abdullahi (Kebbi North), da Senator Garba Musa Maidoki (Kebbi South)