Friday, December 5
Shadow

Me ake nufi da kwaila

Kwaila na Nufin mace sabuwar Balaga amma wadda bata gama mallakar hankalin kanta ba.

Kwailanci na farawa ne daga shekaru 15 har zuwa 18 ko 19.

A tsakanin wadannan shekaru kwaila bata iya magana ba, ko saurayi ta yi, saidai yayi hakuri da ita yayi ta dorata a hanya har ta zama ta fahimci rayuwa. Duk da dai akwai kwailaye da basu da yawa masu hankali.

Hakanan a tsakanin wadannan shekaru, Kwaila na da kaguwa akan abubuwa, musamman ma soyayya, takan bayar da zuciyarta gaba daya idan ta samu saurayi me sonta.

To shiyasa a daidai wannan lokaci idan aka samu mara Imani ya gudu ya barta, zata ji kamar ta yi hauka, zata yi kunci sosai da kuka me tsanani.

Karanta Wannan  Abubuwan dake kara dankon soyayya

Yawanci kwaila bata damu da kudi ba, ko nawa ka bata zata gode maka, abinda ta fi damuwa dashi shine, wannan kulawar da kake bata da kuma shaukin sonka da take ji a zuciyarta wanda bata sababa.

Shiyasa yana da kyau ace kwaila idan so samu ne ta samu saurayi me hankali me wanda suke sa’anni ba. Saboda idan sa’anta take soyaya dashi yawanci hauka zasu yi ta yi, babu wanda zai dora wani akan hanya.

Kwaila na bukatar kulawa sosai, musamman daga wajan danginta watau iyaye, da yayyenta, saboda a wannan tsakani, komai zai iya faruwa da ita.

A nuna mata muhimmancin kanta da darajar kanta, sannan da iya magana, ya zama ba wai a wajan saurayi ko kawayene zata koyi wadannan abubuwan ba.

Karanta Wannan  Addu'a ga masoyiyata

Saidai Kash, yawanci kwailaye suna karewane da koyan wadannan abubuwa a wajan samari da kawayensu, saboda ba kowane iyaye da yayye ne ke tsayawa su kula dasu ba.

Idan ke Kwailace, Ki Sani cewa, duk Duniya babu namiji me sonki fiye da mahaifinki, hakanan babu mace me sonki fiye da mahaifiyarki, dan haka kada dadin kalaman Saurayi yasa ki aikata abinda bashi kenan ba.

Kuma ki sani cewa, zaki iya canjawa soyayyarku akala, idan dai da gaske sonki yake ba kawai dama yaudararki ya zo yi ba, idan saurayinki yana miki abubuwan da baki so, ko kika lura na bata tarbiyyane, ki gaya masa baki so, ki nuna masa bacin ranki, ba tare da cin zarafi ba.

Karanta Wannan  Hoto:Allura cikin ruwa, wannan zankadediyar budurwar 'yar Najeriya dake zaune a kasar Amurka na neman Mijin aure, tace me ilimi take so wanda ya iya girki, dan tana aiki ita zata rike gidan, kuma dole ya iya tsaftace gida sannan dole ya zama gwarzo ne wajan kwanciyar aure

Idan yakiya, wannan sai ki rabu dashi.

Kada ki biyewa kawa ku aikata abinda bashi kenan ba, idan wata larura ta sameki iyayenki da ‘yan uwanki ne zasu rika wahala dake, ba kowace kawa ce zata tsaya dake ba a yayin da wahala ko wata jarabawa ta sameki ba.

Kuma ki kiyayi bayyanawa Saurayi ko kawarki sirrinki, akwai yiyuwar zasu iya cin amanarki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *