
Dan tsohon Gwamnan Kaduna, Bello El-Rufai ya bayyana goyon bayansa ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben 2027.
Hakan na zuwane yayin da mahaifinsa, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ke jam’iyyar SDP da kuma shan Alwashin sai ya kayar da Tinubu daga kan Mulki.
Bello Wanda dan majalisar wakilai ne me wakiltar Kaduna ta kudu, na daga cikin wanda suka halarci babban taron jam’iyyar APC inda jam’iyyar ta bayyana shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a matsayin dan takararta na shekarar 2027.
A watan Maris da ya gabata ne dai El-Rufai ya bayyana cewa ya fice daga jam’iyyar APC saboda a cewarsa ta bar turbar da aka kafata akai.
Reno Omokri da yake mayar da martani kan lamarin yace idan har El-Rufai ba zai iya jawi hankalin dansa ya bar Tinubu ba ta yaya zai iya jawo hankalin ‘yan Najeriya?
A baya dai, dayan dan El-Rufai, Bashir ya caccaki Gwamnan jihar Kaduna, Malam UBA Sani da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.