
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, masu karamin karfi ne zasu sayarwa da gidaje 753 data kwace daga hannun tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele.
Hukumar EFCC ta bayyana cewa wannan gidaje shine kadara guda daya mafi girma da suka taba kwacewa a hannun barawon Gwamnati.
Tuni dai hukumar ta EFCC ta mika wadannan gidaje ga ma’aikatar kula da gidaje da ci gaban birane ta tarayya.