
Rahotanni sun bayyana cewa, kasar Canada na shirin tsaurara matakai na daukar ‘yan kasashen waje aiki a kasar dake zuwa Cirani.
Hakan na nufin ‘yan kasashen waje da yawa dake aiki a kasar na fuskantar barazanar korarsu zuwa kasashen su, ciki hadda ‘yan Najeriya.
Kasar Canada din tace a yanzu kaso 10 cikin 100 ne kawai na ma’aikatan kamfanoni za’a rika barin ana daukar ‘yan kasashen waje inda sauran ‘yan asalin kasar Canada din za’a dauka.
Dan hakane dole a yanzu kamfanonin kasar zasu rage ma’aikatansu wanda ba ‘yan asalin kasar ba da maye ‘yan asalin kasar.