
Rahotanni dake fitowa daga babban birnin tarayya Abuja na cewa, Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayar da umarnin a kulle sakatariyar jam’iyyar PDP ranar Litinin.
Ministan ya bayyana cewa za’a kulle sakatariyar ne tare da wasu gine-gine guda 4,793 da lasisin su ya kare kuma aka kwace.
Hakan na zuwane a yayin da jam’iyyar ta PDP ke shirin babban taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ranar 27 ga watan Mayu.
Tsama tsakanin Wike da jam’iyyar PDP ta barkene bayan da Wike yayi rashin nasara wajan samun tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar a shekarar 2023.
Inda tun wancan lokaci ne ya kudiri aniyar yakar duk wani tsari na Atiku Abubakar.