Friday, December 5
Shadow

Tun ba’a je ko ina ba, Riciki ya kunno kai a jam’iyyar ADC da su Atiku da Peter Obi ke son komawa dan kwace mulki a shekarar 2027

Rahotanni na cewa, riciki ya kunno kai a jam’iyyar ADC da su Atiku da Peter Obi ke son amfani da ita dan tsayawa takarar sugaban kasa a shekarar 2027.

Rahotanni sun ce jam’iyyar a asirce ta canja kundin tsarin mulkinta inda ta baiwa sabbi da tsaffin membobinta dama iri daya, ana tunanin ta yi hakanne saboda manyan ‘yan siyasa irin su Atiku dake shirin komawa cikinta.

Saidai wasu tsaffin ‘yan jam’iyyar sun ki amincewa da wannan mataki inda suka ce ba zasu baiwa kowa mukaman sa suke rike dashi ba musamman wadanda suka shiga jam’iyyar daga baya.

Saidai wasu ‘yan jam’iyyar wanda basu da yawa sun amince da wannan mataki.

Karanta Wannan  Tinubu zai halarci bikin rantsar da sabon fafaroma

Ana tunanin ‘yan Jam’iyyar Adawa zasu yi amfani da jam’iyyar ADC dan yakar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a shekara 2027.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *