Monday, April 6
Shadow

Real Madrid ta sanar da ɗaukar Alonso a matsayin sabon kocinta

Real Madrid ta sanar da ɗaukar Xabi Alonso a matsayin sabon kocinta.

Alonso wanda ya buga wa Real ɗin wasa 236 a matsayin ɗan wasanta a baya, ya saka hannu kan kwantiragin shekara uku.

A farkon watan nan ne ya sanar da cewa zai bar Bayer Leverkusen da yake jagoranta.

Tsohon ɗan wasan na Liverpool da kuma Sifaniya, ya jagoranci ƙungiyar lashe kofin Bundesliga a bara ba tare da an doke shi ko da wasa ɗaya ba – da kuma German Cup.

Alonso wanda yarjejeniyarsa za ta kai har 30 ga watan Yunin 2028, zai maye gurbin Carlo Ancelotti.

Ancelotti ya jagoranci wasansa na karshe a Madrid a ranar Asabar, inda a yanzu zai zama sabon kocin ƙasar Brazil.

Karanta Wannan  Me kamfanin sayar da mota yace zai baiwa Nafisa Abdullahi data lashe gasar Turanci ta Duniya kyautar Naira Dubu dari biyar

Za a gabatar da Alonso wanda ya lashe Champions League a 2014 lokacin da yake buga wa Madrid kwallo – a gobe Litinin a filin atisayen ƙungiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *