Monday, December 16
Shadow

Shekara ɗaya maƙiya Kano su ka yi su na cin dunduniyar gwamnatin Abba, Cewa Kwankwaso

Madugun Kwankwasiyya kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya zargi ‘yan adawa a Kano da cin dunduniyar gwamnatin gwamna Abba Kabir Yusuf har tsawon shekara guda.

Kwankwaso ya fadi haka ne a lokacin da gwamnatin Kano ta ayyana dokar ta-baci kan ilimi a jihar Kano a yau Asabar.

Ya ce, “Bari in fara da taya shi murnar wannan rana mai cike da tarihi, ranar da gwamna ke ayyana dokar ta-baci kan ilimi. Sanin kowa ne cewa gwamna yana aiki tun daga ranar da ya hau mulki a ko’ina a fadin jihar.

“Duk da cewa gwamnan ya na fuskantar kalubale tsawon shekara guda. Nan da nan bayan zaɓe, maƙiyan Jiha sun kai shi Kotu, zuwa Kotun Daukaka Kara zuwa Kotun Koli. Mun ga abin da ya faru duk da sun san cewa babu bukatar a je wata Kotu. Kowa ya san cewa ya ci zabensa.

Karanta Wannan  Gwamnati ta sake kara farashin man fetur zuwa Naira 1070 akan kowace lita

“Hatta makiya suna cewa suna son su karbi mulki da karfin tsiya saboda sun yi imanin cewa suna da gwamnati. Duk da haka, gwamnan ya rika fuskantar kalubale iri-iri, ba mu san abin da ke faruwa ba, kuka abin da ke faruwa a jihar nan shine gwamnan yana aiki.

“A gaskiya wannan ya tuna min halin da na shiga a wa’adina na biyu da watanni biyu da rantsar da ni a matsayin gwamna, mu ka fara fuskantar hare-haren Boko Haram a masallatai, ana kai hare-hare a kasuwanni, ofisoshin ‘yan sanda, makarantu da sauran su, amma mu ka mayar da hankali mu ka tabbatar da cewa ba mu shagala ba,” in ji Kwankwaso.

Karanta Wannan  Shekaru 18 da suka gabata Shugaban Tinubu yaso gina matatar man fetur a Legas>>Dangote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *