Hotuna: Kwamishinan yan sandan Kano ya ziyarci ofishin yan sanda da aka kona a Rano.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, tare da Shugaban Karamar Hukumar Rano, Hon. Mallam Mohammed Naziru Ya’u, sun kai wata ziyara ta gaggawa domin tattara bayanai kai tsaye a caji ofis din ‘yan sanda na Rano da ke Karamar Hukumar Rano a Jihar Kano.
Ziyarar na zuwa ne sakamakon mummunan hari da wasu da ba a tantance ba suka kai a safiyar Litinin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum guda tare da lalata wasu sassa na ofishin ‘yan sanda a Rano.
Kwamishinan ‘Yan Sanda ya ce wannan ziyara na cikin matakan bincike da tabbatar da tsaro a yankin. Ya kuma jaddada cewa rundunar ‘yan sanda tana daukar duk matakan da suka dace domin gano wadanda suka aikata wannan aika-aika da daukar matakin doka a kansu.
Facebook/Abdullahi Haruna Kiyawa