Friday, December 5
Shadow

YANZU-YANZU: Kakakin Majalisa Tajudeen Abbas Ya Janye Kudirin Tilasta Zaɓe wanda za’a rika cin mutum tarar Naira dubu dari bayan da ya sha suka

Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, ya janye kudirin dokar da ke neman tilasta wa ‘yan Najeriya kada kuri’a a kowane zaɓe.

Kudirin dai na neman gyara Dokar Zaɓe ta 2022, inda aka tanadi cewa duk masu cancantar kada kuri’a dole ne su fito su zaɓa a kowanne zabe, kuma wanda ya ki, zai iya fuskantar hukunci na daurin watanni shida zuwa tara, ko tara har Naira 100,000.

Sai dai, wannan kudiri ya jawo ce-ce-ku-ce daga jama’a da kungiyoyin kare hakkin dan adam. Kungiyar SERAP ta bayyana cewa wannan yunkuri ya sabawa yancin dan adam, kundin tsarin mulki da kuma dokokin kasa da kasa. Sun jaddada cewa ‘yancin kada kuri’a yana nufin mutum na da damar yanke shawara – ya kada kuri’a ko kuma ya ki. Haka kuma, sun yi barazanar daukar matakin shari’a idan aka amince da kudirin.

Karanta Wannan  Duka da zagin me laifi baya cikin aikin ku>>Hukumar 'Yansandan Najeriya ta gayawa 'yansandan

Fitattun lauyoyi kamar Awa Kalu (SAN) da Babatunde Fashanu (SAN) sun bayyana rashin dacewar kudirin, inda suka ce dimokuradiyya na bukatar ‘yanci, ba dole ba. Fashanu ya bayyana kudirin da “abin dariya”, yayin da Kalu ya ce kada kuri’a hakki ne, ba wajibi ba.

Masu suka sun ce maimakon tilasta mutane su fito zabe, ya fi dacewa a magance matsalolin da ke hana su fitowa, kamar tsaro, rashin amincewa da tsarin mulki da kuma damuwa da rashin ingantaccen shugabanci.

Biyo bayan wannan martani daga al’umma da kwararru, Kakakin Majalisar ya sanar da janye kudirin, yana mai cewa hakan na zuwa ne bayan dogon nazari da tuntuba kan yadda al’umma ke kallon lamarin a halin yanzu.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon fada a tsakiyar titin babban birnin tarayya Abuja inda mutum daya ya doke mutane 3 ya dauki hankula

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *