Friday, December 5
Shadow

Mutanen da ambaliyar ruwa ta kàshè a Neja sun kai 200, in ji jami’ai

Mutanen da ambaliyar ruwa ta kashe a garin Mokwa na jihar Neja sun kai sama da 200, in ji jami’ai.

Akwai wasu kusan 500 da ba a gani ba har yanzu, yayin da ake ci gaba da aikin ceto.

Mataimakin shugaban karamar hukumar Mokwa, Musa Kimboku ya shaida wa BBC cewa an dakatar da aikin ceto saboda hukumomi sun yi imanin cewa watakila babu wanda ya rage da rai.

Ambaliyar wadda aka bayyana cewa ba a ga irinta ba tsawon shekara 60, ta lalata gidaje a anguwannin Tiffin Maza da Hausawa, bayan tafka mamakon ruwan sama ranar Laraba da daddare.

Hukumomi za su fara tono gawawwaki da aka binne don bincike, a wani yunkuri na kauce wa yaɗuwar cutuka, kamar yadda Maigarin Mokwa Muhammad Aliyu ya bayyana.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo Da Duminsa: Shugaba Tinubu ya isa wajan taro a Birnin Tokyo na kasar Japan

Mazauna yankin sun bayyana cikin kaɗuwa yadda suna kallo suka rasa ƴan uwansu da gidajensu bayan da ruwa ya tafi da su.

Wani mai suna Adamu Yusuf, ya ce ya rasa matarsa da kuma jaririnta.

“Ina ji ina gani har ruwa ya tafi da su babu yanda na iya. Na samu tsira ne saboda ina iya yin iwo,” ya faɗa wa BBC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *