
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, basa sacewa ko yin Almubazzaranci da kudaden da aka ciwo bashi.
Shugaban ya bayyana hakanne a ta bakin kakakinsa, Bayo Onanuga.
Inda ya kara da cewa, kudaden da suke ciwo bashi ya zama dole saboda mafi yawanci ayyukan titi da sauran wasu basa cikin kasafin kudi, yace dan haka dole a ciwo bashi.
Yace kuma ba Najeriya ce kadai kasar dake ciwo bashi ba, hatta kasashe manya irin su Amurka na ciwo bashi.