Mutumin Bauchi Zai Kai Ragon Sallah Gidan Tinubu A Legas Bayan Yunkurin Da Bai Kai Ga Nasara Ba.

Khamis Musa Darazo, wani masoyin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu daga jihar Bauchi, ya shirya kai wa shugaban kasa ragon Sallah a Legas a matsayin alamar godiya bisa amincewar da ya yi da lasisin hakar mai a Kolmani.
A wata hira da aka yi da shi ranar Litinin, Khamis ya shaida wa Vanguard cewa bayan tattaunawa da dattawa, ya yanke shawarar kai ragon zuwa jiharsa ta asali — Legas, da fatan zai samu damar saduwa da shugaban ko wakilansa kafin bikin Sallah.
Khamis ya fara kokarin kai ragon ne ta ofishin jam’iyyar APC a Bauchi, amma an hana shi shiga. Saboda haka yanzu yana fatan gabatar da ragon a Legas, a matsayin alamar godiya ga kokarin shugaban kasa wajen farfado da tattalin arzikin kasa.
Ya ce: “Na fara kokarin aika ragon Sallah ga shugaban kasa Tinubu a matsayin godiya saboda amincewar da ya yi da lasisin Kolmani ta jam’iyyar APC amma abin ya ci tura.
“Daga bisani, bayan na yi shawara da wasu dattawa, sun ba ni shawarar in kai ragon zuwa jihar Legas inda ake sa ran shugaban zai yi bikin Sallah. Ina so kawai in ce ‘na gode’.”
Lasisin mai na Kolmani wani babban aikin hakar mai ne da darajarsa ke kai biliyoyin daloli, kuma yana tsakanin jihohin Bauchi da Gombe. Ana sa ran aikin zai bunkasa tattalin arzikin yankin Arewa tare da samar da guraben aiki.
Khamis na ganin wannan ci gaba zai kawo gagarumin tasiri ga yankin Arewa, don haka yake kokarin nuna godiyarsa.
Wannan ba shi ne karon farko da Khamis ke nuna kauna da biyayya ga shugaban kasa Tinubu ba. A lokacin kamfen dinsa, Khamis ya sadaukar da kudin alawus din hidimar kasa (NYSC) domin tallafa wa tafiyar shugaban.
Baya ga haka, ya sa wa diyarsa suna na mahaifiyar shugaban kasa mariganya, domin nuna girmamawa da kauna ga shugaban da iyalansa.