Friday, December 5
Shadow

Sanata Kalu ya fasakwai inda ya Bayyana masu daukar nauyin Ayyukan tà’àddàncì a Najeriya

Sanata Orji Uzor Kalu dake wakiltar mazabar Abia North a majalisar Dattijai ya bayyana cewa wasu ‘yan siyasa ne da manyan ma’aikatan Gwamnati da ‘yan Kasuwa ke daukar nauyin ayyuka Kungiyar Bòkò Hàràm.

Ya bayyana hakanne a hirar da aka yi dashi a gidan Talabijin na Channels TV.

Yace kuma masu yin hakan suna yi ne dan kawai su hana shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu iya gudanar da Gwamnatinsa yanda ya kamata.

Yace amma ba ta haka bane ake karbar mulki, yace yawanci suna yi ne dan su kwace mulki daga hannun Tinubu ba kudi bane a gabansu.

Karanta Wannan  Bidiyo: Kalli Yanda aka fara gina Kabarin Shugaba Buhari a gidansa dake Daura

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *