
Rundunar sojin Isra’ila ta fitar da sunayen dakarunta uku da ta ce an kashe a arewacin Zirin Gaza ranar Litinin.
Mutanen uku da ke da shekaru 20 da ɗoriya sun fito daga bataliya ɗaya – an ce biyu daga ciki likitoci ne, na ukun kuma kwamanda, a cewar wata sanarwa da rundunar sojin ta IDF ta fitar.
Jaridar Times of Israel ta bayar da rahoton cewa an kashe su ne sakamakon wani bam da ya tashi da su lokacin da suke tsaka da fafatawa da mayaƙan ƙungiyar Hamas a yankin Jabalia.