
Ministan Yada labarai, Muhammad Idris ya bayyana cewa, babu Gwamnatin data samu nasarar da Gwamnatin Tinubu ta samu a shekaru 2 da suka yi suna mulki.
Ya bayyana hakanne a Abuja wajan wani taron karawa juna Sani kan harkar tsaro da wayar da kan ‘yan kasa.
Yace babu gwamnatin data samu nasarar da Gwamnatin Tinubu ta samu a shekaru biyu da suka gabata, da farko dai ya yi maganin masu ci da tallafin man fetur.
Da kuma masu almundahana a harkar canjin Kudi, Ga kuma bashin karatu da yake baiwa dalibai, ga gina Tintuna da sauransu.