
Gwamnatin jihar Legas ta saka tarar naira 250,000 ko daurin watanni 3 a gida gyara hali ga duk wanda aka kama yana zubar da shara ba bisa ka’ida ba.
Kwamishinan Muhalli da ruwa na jihar, Mr. Tokunbo Wahab ne ya fitar da sanarwar ga manema labarai a ranar Talata inda yace masu kunnen kashi wanda aka kama akai-akai zasu fuskanci hukuncin da yafi wannan tsanani.
Hukumar tace tuni aka hukunta mutane 3000 kan wannan lamari inda tace kuma zata ci gaba da hukunta masu laifin.