Wata Mata Ta Cika Da Mamaki Bayan Da Ta Je Duba Gidan Da Ta Ke Ginawa Ta Tarar Wasu Sun Tare A Gidan
Wata mata da take ƙoƙarin gina gidan kanta a Abuja tayi mamaki bayan da ta tarar da wasu hausawa sun tare a gidan da ta ke ginawa a Abuja.
Matar ta ce ta cika da mamaki bayan da ta tarar da mutanen a gidan, wanda bata kammala ginawa ba, su kuma har da gadonsu da kayayyakinsu sun shigar cikin gidan sun tare a ciki.
Ta ce bata damu ba, domin har tukwicin Naira dubu biyu ta basu, lokacin da ta umarce su da su kwashe kayansu su fice daga gidan.