Tuesday, February 3
Shadow

An zane wasu masoya bisa saduwa kafin aure a Indonesiya

An zane wasu masoya bisa saduwa kafin aure a Indonesiya.

An yi wa wani mutum da wata mata bulala ɗari-ɗari kowanne a bainar jama’a a lardin Aceh mai a kasar Indonesia a yau Laraba bayan da wata kotun shari’ar Musulunci ta same su da laifin yin jima’i kafin aure.

An haramta yin jima’i tsakanin masoya da basu yi aure ba a garin na Aceh, wanda ya kafa tsarin shari’ar Musulunci.

Indonesiya ta haramta yin jima’i ba tare da aure ba a sabon kundin dokokin Shari’ah a 2022 amma dokar ba za ta fara aiki ba sai shekara mai zuwa.

Sai dai kuma an yi wa mutanen biyu bulala ɗari-ɗari ta hanyar yin goma-goma a yayin da wasu tsirarun jama’a ke kallo a wani wuri da ke Aceh babban birnin lardin, inda mace ce ta yi wa matar da ake zargin bulala, a cewar wani wakilin AFP da ke wajen da aka yi hukuncin.

Karanta Wannan  Karin Baraka ta kunno kai a jam'iyyar ADC, inda dan majalisa, Leke Abejide yace shima bai yadda da su El-Rufai da Atiku a jam'iyyar ba

Hakazalika an yi wa wasu mutane uku bulala 49 dukkanin su bisa zargin su da yin caca da shan barasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *