Friday, December 5
Shadow

Matashi Daga Jihar Bauchi Zai Nufi Jihar Lagos Ranar Alhamis Domin Ya Je Ya Gwangwaje Shugaba Tinubu Da Ragon Sallah

Matashi Daga Jihar Bauchi Zai Nufi Jihar Lagos Ranar Alhamis Domin Ya Je Ya Gwangwaje Shugaba Tinubu Da Ragon Sallah.

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Khamis Musa Darazo, wani mai kaunar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu daga jihar Bauchi, ya shirya kai ragon Sallah zuwa Lagos domin gabatar da kyautar godiya ga shugaban kasa saboda amincewarsa da lasisin hakar mai na Kolmani.

Khamis ya shaidawa jaridar Vanguard a ranar Litinin cewa, bayan ya tattauna da dattawan yankinsa, ya yanke shawarar daukar ragon zuwa jihar Lagos, inda yake sa ran samun ganawa da shugaban kasa ko wakilansa kafin bikin Sallah.

Khamis ya fara kokarin mika kyautar ragon Sallah din ta ofishin jam’iyyar APC a Bauchi, amma aka hana shi shiga. Yanzu haka yana fatan gabatar da kyautar a Lagos a matsayin alamar godiya bisa kokarin shugaban wajen habaka tattalin arzikin kasa.

Karanta Wannan  Allah Ya Yiwa Alhaji Ali Obobo Da Ya Taba Zuwa Ƙasar Saudiyya Kan Keke Rásųwa

“Na fara kokarin aika ragon Sallah ga shugaban kasa Tinubu don nuna godiya bisa amincewar da ya yi da lasisin hakar mai na Kolmani ta hanyar jam’iyyarsa APC, amma hakan bai yiwu ba.

“Amma bayan shawara da wasu dattawa, an ba ni shawarar kai ragon zuwa jihar Lagos inda ake sa ran shugaban zai yi bikin Sallah. Ina son kawai in ce na gode,” in ji Khamis.

Lasisin hakar mai na Kolmani, wanda ke tsakanin jihohin Bauchi da Gombe, wani babban aikin binciken mai ne mai darajar biliyoyin daloli, wanda ake sa ran zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi a arewacin Najeriya.

Karanta Wannan  Gwamnatin Jihar Legas ta baiwa matashiyarnan da ta so yin Alfasha da maza 100 amma daga baya tace ta tuba jakadiyar yaki da Miyagun Qayoyhi

Khamis yana da yakinin cewa wannan ci gaba zai kawo sauyi mai muhimmanci ga tattalin arzikin yankin, kuma yana fatan nuna godiyarsa.

Ba wannan ne karon farko da Khamis ke nuna kauna da biyayya ga shugaban kasa Tinubu ba.

A lokacin yakin neman zaben shugaban kasa, Khamis ya sadaukar da kudin alawus dinsa na National Youth Service Corps (NYSC) don tallafa wa yakin neman zaben.

Baya ga haka, ya saka wa diyarsa suna daga cikin sunayen iyayen shugaban kasa marigayi, domin nuna irin girmamawarsa ga shugaban da iyalinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *