
Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero yace yayi murna da hana hawan Sallah da hukumar ‘yansandan jihar suka yi.
A ranar Talata ne hukumar ‘yansandan jihar suka fitar da sanarwar cewa, sun dakatar da hawan Sallah a Kano.
Hakan na zuwane jim kadan bayan da sarki Muhammad Sanusi II ya aikawa hakimai da su je hawan Sallah.
Saidai a sanarwar da Sarki Aminu Ado ya fitar yace yana maraba da dakatar da hawan sallar kuma zai bi wannan doka.
Sarki Aminu ya sanar da hakanne ta bakin kakakinsa, Awaisu Abbas Sanusi inda yace ya dauki wannan mataki ne bayan tuntuba da yayi da masu ruwa da tsaki